Nijar: Ba Zan Nemi Wa'adi Na Uku Ba, Inji Isufu
Shugaba Mahamadu Isufu na Jamhuriya Nijar ya yi alkawarin cewa ba zai nemi yin wa'adin mulki na uku ba, kuma babban fatansa shi ne ganin ya mutunta kundin tsarin mulkin kasar.
Wannan dai na nufin Shugaba Isufu ba zai nemi sake tsaywa takara ba a zaben shugabancin kasar na 2021 ba, bayan kammala wa'adin mulkinsa na biyu a jere kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
A shekara 2011 ne Mahamadu Isufu ya dare kan karagar mulkin kasar ta Nijar, kana kuma aka sake zabensa a shekara 2016 data gabata.
Shugaba Isufu ya fada a wata mujjala mai suna ''Marchés africains'' cewa babban fatansa shi ne na ganin ya shirya zabubukan kasar dake tafe kuma ya mika mulki ga wanda al'ummar kasar suka zaba.
Idan hakan ta tabbata Muhamadu Isufu zai kasance wani shugaban kasar ta Nijar na farko cikin tarihi tun bayan samun yancin kai a 1960 da zai shirya babban zabe ya kuma mika mulki ga wanda aka zaba a bisa tafarkin demukuradiya.