Wasu Kasashen Afirka Na Adawa Da Tura Dakarun AU Zuwa Burundi
(last modified Sun, 31 Jan 2016 05:41:24 GMT )
Jan 31, 2016 05:41 UTC
  • Wasu Kasashen Afirka Na Adawa Da Tura Dakarun AU Zuwa Burundi

Shugaban Kasar Gambiya ya bayyana adawarsa da tura dakarun sulhu na kasashen Afirka zuwa kasar Burundi.

Shugaba Yahaya Jammeh ya bayyana haka ne a yayin buda taron kungiyar kasashen Nahiyar Afirka na shekara shekara a jiya Assabar, inda ya ce wasu kasashen Nahiyar Afirka na adawa da tura Dakarun sulhu zuwa kasar Burundi ba tare da amincewar magabatan kasar ba.

Duk da cewa Shugaba Jammeh bai bayyana sunayen kasashen ba, amma ya ce duk wani mataki da kungiyar za ta dauka na tura dakarun sulhu zuwa kasar Burundi ba tare da amincewar magabatan kasar ba, kasar Gambiya na adawa da hakan.

Kwamitin tsaro na kungiyar tarayyar Afirka ya gabatar da shawarar tura Dakarun Sulhu na kungiyar dubu biyar zuwa kasar Burundi domin kawo karshen rikicin kasar.

Rikicin kasar Burundi ya samo asali ne tun bayan da shugaba Nkurinziza ya bayyana aniyarsa na tsayawa takara a karo na uku.inda masu adawa da shi ke ganin cewa kudirin nasa ya sabawa kundin tsarin milkin kasar da kuma yarjejjeniyar sulhu na karo karshen yakin basasa da kasar ta fuskanta a baya.