Nijar : Kungiyoyin Fararen Hula Sun Shiga Da kara Kan Badakalar Urenium
Kungiyoyin fararen hula Jamhuriya Nijar sun shiga da wata kara gaban kotun Yamai, kan badakalar kudaden nan na Urenium.
Jagororin kungiyoyin fararen hular guda biyar sun bayyana ce ya kamata kotun kasar ta maida hankali kan wannan batun na karkata akalar wasu makuden kudaden na urenium daya shafi hamshakin kamfanin Areva na faransa da kamfanin kulda da ma'adunai na kasar Niger Sopamin da kuma ita kanta gwamnatin ta Nijar.
Dama kafin hakan wani kwamiti da majalisar dokokin kasar ta kafa ya fara sauraren wadanda ake zargi a wannan badakala ciki har da ministan kudi na kasar Hasumi Masa'udu.
A bisa ka'ida dai shiga da kara irin wannan gaban kotu zata sa a soke kwamitin da majalisar ta kafa, domin baiwa bangaren shari'a damar gudanar da aikinta, kamar yadda dokokin tsarin mulkin kasar suka tanada.
 
							 
						 
						