Sake gina rundunar tsaron Afirka ta tsakiya
Komandan Cibiyar koyar da dakarun tsaro na Kungiyar Tarayyar Turai ya sanar da taimakawa kasar Afirka ta tsakiya wajen sake gida Rundunar tsaron kasar
Janar Herman Ruys da ya kasance Dan Kasar Belgium kuma Komandan Cibiyar koyar da dakarun tsaro na Kungiyar Tarayyar Turai da ya kai ziyara kasar Afirka ta tsakiya ya bayyana cewa kungiyar tarayyar Turai za ta taimakawa Afirka ta tsakiyan wajen sake gina rundunar tsaron kasar, saboda rikice-rikicen da kasar ta fuskanta tare kuma da takunkumin sayan makamai da aka kakaba mata ya sanya Rundunar tsaron kasar ta yi rauni sosai.
Janar Herman Ruys ya kara da cewa a kwai gungu biyu na Dakarun tsaron kasar Afirka ta tsakiya da kuma adadinsu ya kai dubu biyu za su karbi horo na musaman daga manyan komondojin kungiyar Tarayyar Turai.
Daga Shekarar 2013, zuwa yanzu, kasar Afirka ta tsakiya na fama da yakin cikin gida, kuma duk da cewa an gudanar da zabe a kasar, amma har yanzu sabon shugaban kasar Faustin-Archange Touadéra ya kasa medo da kwanciyar hankali tare da hada kan 'yan kasar.