An hallaka 'yan ta'adda 14 a tsibirin Sinai na kasar Masar
Cikin kwanaki biyu da suka gabata, Dakarun kasar Masar Sun sanar da hallaka 'yan ta'adda 14 a tsibirin Sinai ta arewa.
Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya nakalto Dakarun tsaron Masar na cewa a ci gaba da aikin tsarkake kasar daga 'yan ta'adda Sojojin kasar sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda 14 cikin kwanaki biyu da suka gabata a tsibirin Sinai ta arewa tare kuma da cabke wasu Mutane 21 da ake zarki da alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda, har ila yau Sojojin sun gano maboyar 'yan ta'addar da kuma wasu Motoci biyu gami da makaman yaki masu yawa.
Yankin tsibirin Sinai dai ya kasance tungar kungiyar 'yan ta'addar Ansarul-baitul Makdis da ta kasance wani bangare na kungiyar ISIS a kasar da ya zuwa yanzu suka kai hare-hare da dama kan jami'an tsaron Masar da ma fararen hula a kasar.
A bangare guda, wani Bam ya tashi a cibiyar koyar da aikin 'yan sanda a garin Tanta dake gabashin birnin Alkahira, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar Mutane 16.