Masu Dauke Da Makamai Sun Kashe Fararen Hula Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya
(last modified Wed, 05 Apr 2017 11:20:20 GMT )
Apr 05, 2017 11:20 UTC
  • Masu Dauke Da Makamai Sun Kashe Fararen Hula Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya

Wasu masu dauke da makamai sun kai hari a Ngaoundaye da ke arewa maso yammacin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, wata majiyar tsaro a kasar ta tabbatar da cewa, wannan hari ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula tare da jikkatar wasu, yayin da wasu daruruwa kuma suka tsere zuwa cikin kasar Kamaru.

Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari, amma jami'an tsaro na zargi wasu masu dauke da makamai da ke da alaka da tsohuwar kungiyar tawaye ta Seleka.