An Nada Bruno Tshibala A Matsayin Sabon Firayi Ministan Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19246-an_nada_bruno_tshibala_a_matsayin_sabon_firayi_ministan_congo
Shugaban kasar Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo Joseph Kabila ya nada daya daga manyan 'yan adawa kasar Bruno Tshibala a matsayin sabon Firayi ministan kasar.
(last modified 2018-08-22T11:29:56+00:00 )
Apr 08, 2017 12:07 UTC
  • An Nada Bruno Tshibala A Matsayin Sabon Firayi Ministan Congo

Shugaban kasar Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo Joseph Kabila ya nada daya daga manyan 'yan adawa kasar Bruno Tshibala a matsayin sabon Firayi ministan kasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayanin shugaba Kabila da aka watsa kai a daren jiya a dukkanin tashin talabjin da na radio a kasar Congo, ya sanar da nada Bruno Tshibala a matsayin sabon firayi ministan kasar.

Wannan mataki ya zo ne bisa yarjejeniyar da aka cimmawa tsakanin jam'iyyun adawa da kuma bangaren gwamnati a tattaunawar ad suka yi a karshen watan Disamban 2016, da nufin shawo kan matsalolin siyasa da na tsaro da suka addabi a kasar.