Zanga-Zangar Al'ummar Masar Kan Matsalar Tsaro A Kasar
Al'ummar garin Iskandariyya na kasar Masar sun gudanar da zanga-zangar lumana suna zargin gwamnatin kasar da nuna gazawa a fagen wanzar da zaman lafiya da tsaro a kasar.
Rahotonni daga Masar suna bayyana cewa: Al'ummar garin Iskandariyya da ke arewacin kasar Masar sun gudanar da zanga-zangar lumana a jiya Lahadi a manyan hanyoyin garin domin nuna rashin jin dadinsu kan yadda matsalolin tsaro suke ci gaba da addabarsu dama sauran al'ummar kasar.
Masu zanga-zangar sun toshe manyan hanyoyin garin tare da rera taken daura alhakin tabarbarewan matakan tsaro a kasar kan gwamnatin Masar sakamakon gazawar jami'an tsaron kasar na wanzar da matakan tsaro.
A jiya Lahadi ce dai wasu bama-bamai har uku suka tarwatsa a wasu majami'u biyu na mabiya addinin Kirista da kuma cibiyar horas da jami'an 'yan sanda, inda suka lashe rayukan mutane fiye da 40 tare da jikkata wasu fiye da 100 na daban.