Sharhi: Munanan Hare-Haren Ta'addanci Sun Girgiza Kasar Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19314-sharhi_munanan_hare_haren_ta'addanci_sun_girgiza_kasar_masar
A jiya ne aka kaddamar da wasu hare-haren ta’addanci a garuruwan Tanta da kuma Iskandariyya a kasar Masar, da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 46 tare da jikkatar wasu da dama.
(last modified 2018-08-22T06:59:56+00:00 )
Apr 10, 2017 10:25 UTC
  • Sharhi: Munanan Hare-Haren Ta'addanci Sun Girgiza Kasar Masar

A jiya ne aka kaddamar da wasu hare-haren ta’addanci a garuruwan Tanta da kuma Iskandariyya a kasar Masar, da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 46 tare da jikkatar wasu da dama.

Dukkanin hare-haren biyu dai an kai su ne ta hanyar kunar bakin wake a kan manyan majami’oin mabiya addinin kirista, an kai hari na farko ne a kan babbar majami’ar garin Tanta da ke arewacin birnin Alkahira, inda mutane fiye da 30 suka rasa rayukansu wasu da dama kuma suka jikkata, hari na biyu kuma an kai shi a kan wata babbar majami’a da ke birnin Iskandariyya, inda mutane fiye da 10 suka rasa rayukansu, wasu da dama kuma suka jikkata.

A yammacin jiya shugaban kasar ta Masar Abdulfattah Sisi ya gabatar da wani jawabi, wanda dukkanin kafafen yada labarai na kasar Masar da ma wasu na kasashen ketare suka watsa kai tsaye, inda a cikin jawabin nasa bayan mika ta’aziyya ga al’ummar Masar musamman iyalan wadanda harin ta’addancin ya rutsa da su, Sisi ya sanar da kafa dokar ta baci har tsawon watanni uku a jere a fadin kasar ta Masar, inda ya umarci rundunar sojin kasar ta karbi tsaron muhimman wurare a cikin a kasar.

Haka nan kuma Sisi ya yi ishara da cewa, kawo karshen ayyukan ta’addanci a yankin na bukatar a hukunta wasu kasashe, wadanda bai ambaci sunayensu ba, wadanda ya ce su ne suka kirkiro kungiyoyin ‘yan ta’adda kuma suke daukar nauyinsu da makudan kudade.

Sai dai jim kadan bayan kaddamar da wadannan hare-hare, kungiyar ta’addanci ta ISIS ta sanar da cewa ita ce take da alhakin kai hare-haren.

Wannan dai na daga cikin hare-hare mafi muni da aka kai kasar Masar, tun bayan da aka fara artabu da ‘yan ta’adda masu akidar kafirta musulmi, wadanda suke samun fatawoyi daga malaman wasu kasashen larabawa wajen kai hare-haren ta’addanci da sunan jihadi.

Da dama daga cikin masu harhi kan harkoksin tsaro a  kasar ta Masar suna danganta ta’azzar irin wadannan hare-haren ta’addanci a cikin kasarsu da takun sakar da ake yi tsakanin gwamnatin kasar da kuma gwamnatocin Qatar da Saudiyyah da Turkiya a daya bangaren, tun bayan da Masar taki amincewa da wani daftarin kudiri da wasu kasashen larabawa suka gabatar a gaban kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, da ke neman a dauki matakin soji a kan kasar Syria domin kifar da gwamnatin Bashar Assad, amma Abdulfattah Sisi yaki amincewa da hakan, sakamakon hakan Saudiyya ta janye jakadanta daga kasar Masar, tare da dakatar da sayar wa Masar man fetur mai rahusa da take yi, baya ga haka kuma wasu daga cikin jami’ai a kasar ta Saudiyya suka gargadi Sisi da cewa zai yaba wa aya zaki, sakamakon wanann matsaya da ya dauka.

Baya ga kasar Saudiyya, Abdulfattah Sisi yana takun saka da kasashen Qatar da Turkiya, wadanda su ma suna da babban tasiri a kan kungiyoyin ‘yan ta’adda da suke yaki a Syria da Iraki da kuma Libya, musaman kungiyar ISIS.