Masar Ta yi Suka Ga Kasashen Da Su Ke Kare 'Yan ta'adda.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19380-masar_ta_yi_suka_ga_kasashen_da_su_ke_kare_'yan_ta'adda.
Pira ministan Masar Sharif Isma'ila ya ce; Harin ta'addanci na karshe da aka kai a kasar da akwai hannun wasu kasashen waje.
(last modified 2018-08-22T06:59:57+00:00 )
Apr 12, 2017 14:32 UTC
  • Masar Ta yi Suka Ga Kasashen Da Su Ke Kare 'Yan ta'adda.

Pira ministan Masar Sharif Isma'ila ya ce; Harin ta'addanci na karshe da aka kai a kasar da akwai hannun wasu kasashen waje.

Pira ministan Masar  Sharif Isma'ila ya ce; Harin ta'addanci na karshe da aka kai a kasar da akwai hannun wasu kasashen waje.

pira ministan  kasar ta Masar, ya fadi haka ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabi a gabana majalisar dokokin kasar. 

Shi ma shugaban majalisar dokokin ta Masar Ali Abdul aal ya ce; gwmanatin kasar tana da tabbacin cewa harin da aka kai wa majami'u biyu a kasar, 'yan ta'addar sun yi amfani ne da na'urorin sadarwa na zamani haka nan abubuwa masu fashewa da shakka babu wasu kasashe ne su ka bayar da su.

A jiya talata ne dai majalisar dokokin kasar ta amince  da dokar ta baci da aka kafa ta tsawon kwanaki uku a kasar.

A wasu hare-haren ta'addanci da aka kai wa majami'u biyu a Alexandria da kuma TAnta, an kashe mutane fiye da 40 yayinda wasu fiye da 100 su ka jikkata.