An Kama 'Yan Adawa Da Dama A Kasar D/Congo
(last modified Thu, 13 Apr 2017 18:55:07 GMT )
Apr 13, 2017 18:55 UTC
  • An Kama 'Yan Adawa Da Dama A Kasar D/Congo

Shugaban Ofishin kare hakin bil-adama na MDD a Jumhoriyar D/Congo ya sanar da kame dariruwan 'yan adawa a kasar

Shugaban Ofishin kare hakin bil-adama na MDD a kasar D/Congo Koffi Edem Wogomebou ya sanar da cewa a shirin Gwamnatin kasar Congo na hana zanga-zangar kin jinin Gwamnati, Jami'an 'yan sanda sun yi awan gaba da manbobin babbar jam'iyar adawa ta kasar kimanin 132.

Babbar jam'iyar hammayar ta Kasar UDPS ta bukaci Al'ummar kasar da su gudanar zanga-zangar gama gari na kin jin Gwamnatin Joseph Kabila, lamarin da ya sanya Gwamnatin daukan wannan mataki na kame jigogin jam'iyun adawar kasar, a ranar Juma'ar da ta gabata ce Shugaba Kabila ya nada Bruno  Tshibala a matsayin sabon Piraministan kasar, lamarin da ya harzika Jam'iyun hammaya.

'Yan adawar Gwamnatin kasar Congon na shirin rubuta wasika zuwa ga Shugaba Kabila kan yadda za a zartar da yarjejjeniyar da suka cimma dangane da kafa Gwamnati bayan rasuwar madugun 'yan adawa, kafin sun tattaunce kwaram sai suka ji an nada Bruno Tshibala a mikamin Piraministan, lamarin da bai yi musu dadi ba.