Amurka Ta Girke Dakarunta A Somalia
Amurka ta sanar da girke wasu gomman dakarunta a Somalia bisa bukatar mahukuntan Mogadisho domin dafawa sojojin kasar yaki da kungiyar Al'shabab.
Wata sanarwa da ofishin sojin Amurka a kasahen Afrika dake da cibiya a Jamus ya fitar an ce dakarun zasu taimakawa sojojin gwamnatin Somalia akan dabarun yaki da ta'addanci.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da Amurka ke jibge dakarunta a Somaliya ba.
A karshen watan Maris da ya gabata gwamnatin Donald Trump ya dau matakin fadada aikin sojin kasarsa wanda zai kai har zuwa kai hari kan mayakan al'shabab dake alaka da Al'Qaida.
A shekara 2016 data gabata sojojin Amurka sun kai hare hare da jiragai marasa matuki kimanin 15 kan 'yan ta'addan na Somalia wanda wasu alkalumma suka ce sun hallaka mutane kimanin 300 galibi 'yan al'shabab a Somaliya