Nijar : Isufu Ya Canza Ministan Ilimi Mai Zurfi, Bisa Bukatar Dalibai
Shugaba Isufu Mahamadu na jamhuriya Nijar ya aiwatar da wani gajeren garen bawul a majalisar ministocinsa inda ya sauya ministan ilimi mai zurfi na kasar Ben Omar kamar yadda daliban kasar suka bukata.
An dai nada Yahuza Sadisu Madubi a matsayin sabon ministan ilimi mai zurfi, inda shi Ben Omar din aka nada shi a matsayin ministan kwadago.
Kungiyar koli ta daliban kasar ce CD/USN ta buga kai ga kasa na cewa sai an tube ministan bayan zanga-zangar da tayi sanadin mutuwar wani dalibi da kuma raunana wasu masu yawa a yayin arangama da jami'an tsaro a ranar 10 ga watan Afrilun nan a Yamai babban birnin kasar.
Firaministan kasar ne Birji Rafini dake jagorantar kwamitin da shugaban kasar ya kafa na sansanta rikicin ne ya gabatarda da shawara canza ministan kamar yadda daliban suka bukata.
Ko baya ga hakan an sallami jagororin kungiyar daliban su gudu hudu da ake tsare da a gidan kurkukun Yamai.
A yanzu dai ya rage a ga ko kungiyar daliban zata gamsu da wannan matakin, wanda ake ganin dai gwamnatin ta nuna da gaske take akan kawo karshen wannan takaddama.