An kashe Mutane 12 a kasar Afirka ta tsakiya
Magabatan kasar Afirka ta tsakiya sun sanar da mutawar mutane 12 a hanun 'yan bindiga da suka hari a wani kauyen kasar
Kamfanin dillancin Labaran Reuteus ya nakalto magabatan kasar Afirka ta tsakiya yau na cewa harin an kai shi a kusa da gariin Banbari dake tsakiyar kasar, inda aka ce rikicin ya kuno kai ne bayan wani sa insa a kan dabobi, bayan haka rikicin ya rikide ya koma na kabilanci tsakanin kabilar peuhl da kabilan Fulani.
Sanarwar ta kara da cewa wannan rikici ba shi da alaka da rikicin siyasa ko na Addini da ya fara tun daga shekarar 2013 wanda ya lakume duban rayuka tare da raba wasu dubai na daban da gidajensu.
Magabatan sun ci gaba da cewa a jiya ma an kai wasu hare-hare a wasu kauyukan kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 6.
wannan dai shine rikici na biyu tun bayan da aka rantsar da Faustin-Archange Touadera a matsayin sabon shugaban kasar a daren Talatan da ta gabata, bayan zaben da aka gudanar wanda yake cike da kyakyawan fata na kawo rikicin kasar.