Azhar Da Vatican A Shirye Suke Su Yi Yaki Da Ta'addanci
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19744-azhar_da_vatican_a_shirye_suke_su_yi_yaki_da_ta'addanci
Cibiyar Azhar ta kasar Masar ta sanar da cewa a shirye take ta hada karfi da karfe tare da fadar vatican wajen yaki da ayyukan ta'addanci da ake aikatawa da sunan addini.
(last modified 2018-08-22T07:00:00+00:00 )
Apr 24, 2017 02:20 UTC
  • Azhar Da Vatican A Shirye Suke Su Yi Yaki Da Ta'addanci

Cibiyar Azhar ta kasar Masar ta sanar da cewa a shirye take ta hada karfi da karfe tare da fadar vatican wajen yaki da ayyukan ta'addanci da ake aikatawa da sunan addini.

Kamfanin dillancin labaran Rasa ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ya fitar a jiya, mataimakin babban malamin Azahar sheikh Abbas Shauman ya bayyana cewa, Azhar tare da fadar Vatican, a matsayinsu na manyan cibiyoyin addinan muslunci da kiristanci a duniya, za su yi aiki tare wajen yaki da duk wani ta'addanci da ake aikatawa da sunan wadannan addinai biyu.

Bayanin ya ce, hanyoyin da bangarorin biyu za su bi sun hada da wayar da kai, da kuma bayyana hakikanin koyarwar addinansu ta zaman lafiya.

Haka nan kuma ya yi ishara da ziyarar Paparoma Francis a kasar masar da cewa, hakan ya kara tabbatar da irin kyakyawar dangantaka da ke tsakanin mabiya addinan biyu.