Rikicin Siyasa Yana Ci Gaba Da Lashe Rayukan Mutane A Kasar Burundi
Rikicin siyasa yana ci gaba da lashe rayukan mutane a kasar Burundi duk da matakan matsin lamba da gwamnatin kasar ke fuskanta daga kungiyoyin kasa da kasa.
Rahotonni daga Burundi suna bayyana cewa: A karshen makon da ya gabata akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu a ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da ake kai wa a sassa daban daban na kasar.
Rahotonnin sun fayyace cewa: A yammacin ranar Asabar da ta gabata; sojojin gwamnatin Burundi sun harbe wani farar hula har lahira mai suna Jean Claude Bashirahishize mazaunin yankin Rukina da ke karamar hukumar Mukike a birnin Bujumbura fadar mulkin kasar. Kamar yadda majiyar 'yan sandan kasar ta sanar da gano gawar wani direba mai suna Asmane Nduwimana a kudancin yankin Kanyosha da ke birnin na Bujumbura da barayi suka kashe bayan sun kwace motarsa a ranar Lahadin da ta gabata. Haka nan a ranar Lahadin an gano gawawwakin wasu mutane biyu daya daga cikinsu mace a lardunan gabashi da kuma na kudancin birnin Bujumbura fadar mulkin kasar.
A yau Talata 25 ga watan Aprilu shekara ta 2017 kasar Burundi ke cika shekaru biyu da bullar rikicin siyasa tun bayan da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya yi tazarce a kan karagar mulki a matsayin wa'adi na uku, duk da cewa kundin tsarin mulkin kasar ta takaita wa'adin shugabanci biyu ne kacal ga duk wani shugaba a kasar.