Sojojin Amurka Sun Fara Ficewa Daga Kasar Afrika Ta Tsakiya
Majiyar sojojin Amurka a nahiyar Afrika wato AFRICOM ta bayyana cewa sojojin Amurka da suke gabacin AFrika ta tsakiya sun fara janyewa daga kasar.
Kamfanin dillancin labaran kasar faransa AFP ya nakalto Charles Chuck Prichard babban komandan sojojin AFRICOM yana fadar haka a yau Laraba. Ya kuma kara da cewa zuwa karshen watan satumba na wannan shekara dukkan sojojin Amurka da suke gabacin kasar Afrika ta tsakiya zasu fice daga yankin.
A shekara ta 2011 ne gwamnatin Amurka ta lokacin ta aike da sojoji 100 zuwa gabacin Afrika ta tsakiya da nufin yakar kungiyar Lord risistance Army ta kasar Uganda. Sai kuma a shekara ta 2015 ta kara sojojin sama 150 a yankin.
Tun shekara ta 1988 yan tawayen Lord Risidtance Army suka fara yakar gwamnatin Yoweri Museveni ta kasar Uganda wanda hakan ya jefa kasar cikin ayyukan take hakkin bil'adama masu yawa.