Amurka Ta Mayar Wa Jonathan Martani Kan Dalilin Faduwarsa Zaben 2015
Ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya yayi watsi da zargin da tsohon shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan na cewa gwamnatin Amurka karkashin jagorancin shugaban shugaban kasar Barack Obama tana da hannu cikin shan kayen da yayi a zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekara ta 2015
Kafafen watsa labarai a Nijeriyan sun ce kakakin ofishin jakadancin Russel Brooks ne ya bayyana hakan inda ya ce Amurka dai tana kira ne zuwa gudanar da zabe mai inganci ba tare da wani magu-magu ba. A saboda haka sakamakon zaben na Nijeriya yana nuni ne da ra'ayin al'ummar Nijeriyan, don haka Amurka ba ta da hannu cikin hakan.
Tsohon Shugaba Jonathan din yayi wannan zargi na sa ne cikin wani littafi mai suna "Against The Run of Play" wanda wani fitaccen dan jaridar This Day, Olusegun Adeniyi ya wallafa inda ya ce shugaba Barack Obama da jami'an gwamnatinsa sun bayyana masa a fili cewa suna son sauyin gwamnati a Nijeriya saboda zarginsa da suke yi da daure wa rashawa da cin hanci gindi a kasar, yana mai cewa shugaba Obama ya hada baki da firayi ministan Birtaniyya na lokacin David Cameroon da kuma shugaban Faransa Francois Hollande don cimma wannan manufa.
Har ila yau a cikin littafin dai shugaba Jonathan ya zargin shugaban hukumar zabe na Nijeriya (INEC) na lokacin Farfesa Attahiru Jega da kuma shugaban jam'iyyarsu ta PDP na lokacin Alhaji Ahmad Adamu Mu'azu da hannu cikin makircin kafa da shi a zaben na 2015 lamarin da tsohon shugaba PDP din ya musanta.