Shugaban Kasar Nijer Ya Jadadda Aniyarsa Na Yaki Da Ta'addanci.
Shugaban Kasar Nijer Ya Jadadda aniyarsa na kalubalantar barazanar ta'addanci a yankunan dake kan iyakokin kasar
A cikin wani Jawabi da ya gabatar a wannan Juma'a, Shugaba Isoufou Mahamadou na kasar Nijer ya bayyana cewa kasar sa na da iyaka da kasashen Libiya, Mali da kuma yankin tekun Tchadi kuma dukkanin wadannan yankuna na fama da 'yan ta'adda, domin haka kasar na bukatar hadin kan Al'ummar kasar baki daya domin tunkarar wannan barazana.
Tun a shekarar 2009 ne dai kungiyar Boko haram ta fara kai hare-haren ta'addanci a arewacin Najeriya, a shekarar 2015 kungiyar ta fadada kai hare-haren ta a kasashen Tchadi, Kamaru da Jumhoriyar Nijer.
Daga shekarar 2009 zuwa yanzu, rikicin kungiyar Boko Haram ya yi sanadiyar mutuwar Mutane sama da dubu 20 a kasashen Najeriya, Nijer, Kamaru da Tchadi sannan kuma ya raba wasu sama da milyan biyu da mahalinsu.