Wani Sabon Rikici Ya Barke A Gabashin D/Congo
(last modified Sat, 29 Apr 2017 05:44:12 GMT )
Apr 29, 2017 05:44 UTC
  • Wani Sabon Rikici Ya Barke A Gabashin D/Congo

Fararen hula da dama suka rasa rayukansu sanadiyar barkewar wani sabon rikici a gabashin jumhoriyar Demokaradiyar Congo

Majiyar hukumar 'yan sandar D/Congo sun sanar a jiya juma'a cewa akalla fararen hula 29 ne suka rasa rayukansu a wani sabon rikicin da ya barke tsakanin kungiyar dake dauke da makamai ta Nyatura da kuma mayakan Majalisar tabbatar da tafarkin Demokaradiya a yankin Masisi na Jihar Kivo ta arewa.

Majiyar 'yan sandar Congon ta kara da cewa kungiyoyin 'yan tawayen biyu wato Nyatura da kuma na Majalisar tabbatar da tafarkin Demokaradiya na ciki yaki ne bisa jagorancin manyan Hafsoshin Dakarun kasar da aka kora a arewa maso gabashin kasar.

Sama da shekaru ashirin kenan da yankunan Gabas da kuma arewa maso gabashin kasar Jumhoriyar Congo ke fama da rikici, kuma duk da irin tarun dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD dake aka tura cikin kasar sun kasa wajen kawar da kungiyoyin dake dauke da makamai da kuma tabbatar da tsaro a yankunan arewa maso gabashin kasar.