Shirin Bayar Da Ilimi Kyauta A Kasar Ghana
(last modified Tue, 02 May 2017 05:40:14 GMT )
May 02, 2017 05:40 UTC
  • Yara dake daukan darasi a cikin aji
    Yara dake daukan darasi a cikin aji

Kasar Ghana na shirin bullo da tsarin bayar da ilimi kyauta ga matasan kasar, matakin wanda ake ganin zai yi tasiri ga makomar milyoyin matasan kasar.

Shugaban kasar ne Nana Akufo-Addo, ya bijiro da shirin kamar yadda ya sha alwashin yi, a lokacin yakin neman zabensa.

Ana ganin cewa wannan tsari zai kawo sauyi ga rayuwar miliyoyin matasa musamman ma 'yan mata da ke fuskantar babban kalubale da karanci wajen shiga makarantun boko, sannan zai bada damar yaki da talauci, da kuma tsarin bunkasa kasa. 

A kasar Ghana dai shiga makarantun sakandari ya wajaba ne daga cin jarabawa a matakin farko, sannan ga adadin guraben da ake bukata, sai kuma idan iyayen za su iya biyan kudadan karatun 'ya'yan su.

A watan daya gabata shugaba Akufo-Addo ya jaddada akan ganin an kai ga samar da wannan tsarin, wanda ya yi ammanar cewa zai taimaki 'yan mata wajen samun ilimin boko mai nagarta da kuma samar da ci gaban kasar.

Nana Afuko Addo ya kara da cewa, ''samar da ilimi mai kyawo ga diya mata yana da mahimmanci sosai idan muna bukatar kawar da talauci, jahilci, mayan cutukan dake addabar kasarmu'' 

A halin da ake ciki zunzurutan kudade Miliyan 400 na kudin Ghana wato (Cedes) kwatamcin Miliyan 88 na Yuro (Euro) ne aka warewa shirin a cikin kasafin kudin kasar na wannan shekara ta 2017. 

Wani rahoto da MDD ta fitar a shekara 2015 ya nuna cewa a kasar Ghana diya mata na zamen makarantun boko na kusan tsawan shekaru 6 yayin da samari maza ke yin kusan shekaru 8, kwatamcin tazara ta shekara biyu tsakaninsu.

Duk da hakan wadannan alkalumen sun kasance abun azo- a- gani idan aka kwatamtasu dana sauren kasashen Afrika na kudu da hamadar sahara 

Wasu alkaluma da asusun kula da yara kankana na MDD wato UNICEF ya fitar a cikin shekarun 2008 zuwa  2012 sun nuna cewa kusan yara 85% a kasar Ghana ana sa su kananan makarantun firamari amman kashi 44% ne kawai suka shiga matsakaitun makarantun sakandare a yayin da kason maza ke zamen kashi 48%.

Wani bincike na kungiyar hulda da ci gaban tattalin arziki ta OCDE ya nuna cewa idan matasa 'yan kasa da shekara 15 sun samu ilimi na tun tashin farko hakan zai habaka tattalin arzikin kasa da dugu uku sakamakon taimakon da zasu kawowa cikin iyalansu.

Sannan kuma samun ilimi zai taimaka wajen kaucewa daukan juna biyun da ba'a shirya ma ba, da kuma rage yawan mace-macen mata wajen haihuwa.

Kasar Ghana dake matsayin kasa ta biyu mafi tattalin arziki a yammacin Afrika bayan Najeriya, ta bada sakamako mai kyawo wajen inganta sha'anin ci gaban al'umma, inda a tsakanin shekara 1992 zuwa 2013 kasar ta rage rabin yawan al'ummarta dake rayuwa a cikin talauci daga kashi 50 zuwa 25%.