Wasu 'Yan Bindiga Sun Kashe Sojojin Gwamnatin Niger A Yankin Yammacin Kasar
(last modified Wed, 03 May 2017 16:52:25 GMT )
May 03, 2017 16:52 UTC
  • Wasu 'Yan Bindiga Sun Kashe Sojojin Gwamnatin Niger A Yankin Yammacin Kasar

Gwamnatin Jamhuriyar ta tabbatar da cewa: Wasu gungun 'yan bindiga sun kai farmaki tare da kashe sojojin kasarta biyu a yankin yammacin kasar.

Gwamnatin Jamhuriyar Niger ta tabbatar da cewa: Wasu gungun 'yan bindiga sun kai hari kan wani wajen binciken ababan hawa a garin Folneko da ke jihar Tilabery kusa da kan iyakar kasar da kasashen Mali da Burkina Faso a daren Lahadi wayewar garin Litinin, inda suka kashe sojojin Niger biyu.

Rahotonni sun bayyana cewa: Bayan kaddamar da harin kan sojojin na Niger sun kuma dauki matakin yin awungaba da wasu makamai da na'urori gami da babura biyu.

A ranar 6 ga watan Maris da ya gabata ma irin wannan harin wuce gona da irin kan jami'an tsaron Niger ya lashe rayukan sojojin gwamnatin kasar biyar a yankin garin na Tilabery da ke arewa maso yammacin kasar.