An Hallaka Sojin Amurka A Somaliya
Wani sojin Amurka guda ya hallaka a wani yanki dake yammacin birnin Magadushu fadar milkin kasar Somaliya
Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto cibiyar Dakarun tsaron kasar Amurka dake Somaliya ta sanar a wannan Juma'a cewa cikin wani farmakin hadin gwiwa da suka kaiwa mayakan Ashabab a yammacin birnin Magadushu jami'in ta guda ya rasa ransa.
A cikin shekarun baya bayan nan kasar Amurka ta sake tura wani adadi na jami'an ta da suka hada da masu bayar shawara kan harakokin tsaro zuwa kasar ta Somaliya, kuma bayan hawan Shugaba Donal Trump kan karagar milki ya tabbatar da irin rawan da Dakarun kasar sa ke takawa wajen yaki da kungiyar Ashabab a Somaliya.
Saidai a bangare guda magabatan kasashen Afirka sun yi gargadi kan mumunan tasirin jami'an tsaron Amurka a yakin da kungiyar Ashabab a Somaliyan.
A shekarar 1993 Amurka ta kwashe Sojojin ta daga kasar Somaliyan bayan da aka kakkabo jiragen yakin ta biyu a birnin Magadushu kafin daga bisani a shekarun baya bayan a sake tura wasu na daban da suka hada da masu bayar da shawara kan harakokin tsaro.