Kwararar 'Yan Gudun Hijira Daga Afirka Ta Tsakiya Zuwa Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.
Radiyo Okabi na Kasar Demokradiyyar Congo ya ambato majiyar tsaron Afirka ta tsakiya na cewa; dubban mutane ne su ke kwarara saboda kaucewa rikicin da kasar ta ke fama da shi.
Radiyo Okabi na Kasar Demokradiyyar Congo ya ambato majiyar tsaron Afirka ta tsakiya na cewa; dubban mutane ne su ke kwarara saboda kaucewa rikicin da kasar ta ke fama da shi.
Jami'in tsaron na gundumar Bas-Ulele na kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, Bangi Bangi ne ya sanar da shigar 'yan gudun hijirar wanda ya fara daga ranar talata ta makon da ya gabata, wanda kuma ya ke ci gaba har yanzu.
A can kasar ta Afirka ta tsakiya ana ci gaba da samun taho mu gama a tsakanin kungiyoyin Silika da kuma Anti Balaka wanda ya ke tilastawa mutane ficewa daga kasar.