An Tube Shugaban Jami'ar Azhar Ta Kasar Masar Daga Kan Mukaminsa
Sheikh Ahmad Tayyib ya tsige shugaban jami'ar Azhar ta kasar Masar daga kan mukaminsa sakamakon kafirta wani manazarci da yayi saboda sabanin mahanga.
Kafafen watsa labaran Masar a jiya Asabar sun habarta cewa: Sheikh Ahmad Tayyib babban jagoran cibiyar nazarin addinin Musulunci ta kasar Masar wato Jami'ar Azhar ya bada umurnin tsige shugaban jami'ar ta Azhar Ahmad Hasani Taha daga kan mukaminsa tare da maye gurbinsa da Sheikh Muhammad Husain Al-Maharsawi shugaban bangaren koyar da harshen larabci na jami'ar a matsayin shugaba na rikon kwarya.
Sheikh Ahmad Hasani Taha dai ya kafirta Islam Buhairi ne wani manazarci a kasar ta Masar kan zargin cewa Islam Bukhari yana gurbata tunanin al'ummar kasar tare da kawar da su daga kan hakikanin koyawar addinin Musulunci, amma bayan nan Sheikh Ahmad Hasani Taha ya janye furucinsa kan Islam Buhairi tare da neman uzuri kan batancin da yayi kansa.
A cikin watan Disamban shekara ta 2015 wata kotu a kasar ta Masar ta zartar da hukuncin dauri a gidan kurkuku na tsawon shekara guda kan Islam Buhairi kan zargin muzanta addinin Islama, amma aka sake shi karkashin ahuwar da shugaban kasar ya yi ga wasu daga cikin fursunonin da ake tsare da su.