Ana Zaman Zullumi A Gabashin Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20372-ana_zaman_zullumi_a_gabashin_jamhuriyar_afirka_ta_tsakiya
Wasu 'yan bindiga sun kaddamar da hari a kan dakarun kiyayen sulhu na majalisar dinkin duniya gabashin Jmahuriyar Afirka ta tsakiya.
(last modified 2018-08-22T07:00:06+00:00 )
May 14, 2017 07:45 UTC
  • Ana Zaman Zullumi A Gabashin Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya

Wasu 'yan bindiga sun kaddamar da hari a kan dakarun kiyayen sulhu na majalisar dinkin duniya gabashin Jmahuriyar Afirka ta tsakiya.

Gidan radiyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, daruruwan 'yan bindiga ne dauke da muggan makamai suka kutsa kai a cikin birnin Bangasu da ke kudu maso gabashin jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

Rahoton ya ce 'yan bindigar sun killace wani sansanin dakarun kiyaye sulhu na MDD da ke birnin, inda wasu daga cikinsu kuma suka shiga wawure kaddarorin jama'a, daga bisani suka kuma suka ce daga birnin tare da dukiyoin da suka sace, kamar yadda kuam suka kashe daya daga cikin dakarun MDD.