Nijar: Dubban 'Yan Ci-rani Sun Tsira Daga Mutuwa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20534-nijar_dubban_'yan_ci_rani_sun_tsira_daga_mutuwa
Sojojin Kasar Nijar sun sanar da ceto da 'yan ci ran masu yawa daga hannun masu fasa kwaurin mutane.
(last modified 2018-08-22T11:30:08+00:00 )
May 20, 2017 06:23 UTC
  • Nijar: Dubban 'Yan Ci-rani Sun Tsira Daga Mutuwa

Sojojin Kasar Nijar sun sanar da ceto da 'yan ci ran masu yawa daga hannun masu fasa kwaurin mutane.

Sojojin Kasar Nijar sun sanar da ceto  'yan ci ran masu yawa daga hannun masu fasa kwaurin mutane.

Majiyar tsaron kasar Nijar ta sanar a jiya juma'a cewa; Sojojin Kasar sun 'yantar da 'yan ci-rani 40 daga hannun masu fasa kwaurin mutane, akan hanyarsu ta shiga Libya domin isa nahiyar turai.

'Yan ci ranin dai an tseratar da su ne daga hannun 'yan fasa kwaurin a cikin saharar arewacin kasar. Kuma sun fito ne daga kasashen Najeriya, Gambia, Gunea, Senegal, da Nijar.

Ministan harkokin cikin gida, Muhammadu Bazum, wanda ya ziyarci arewacin kasar, ya bada tabbacin daukar matakai domin hana masu fasa kwaurin mutane cin karensu babu babbaka a yankin.