Tseratar Da Bakin Haure 4,400 Daga Halaka A Tekun Mediterranea
Dakarun tsaron gabar tekun Libiya da na Italiya sun samu nasarar tseratar da bakin haure kimanin 4,400 daga halaka a tekun Mediterranea.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya watsa rahoton cewa: Dakarun tsaron gabar tekun Libiya da na Italiya sun yi nasarar tseratar da bakin haure 2,900 daga halaka a tekun mediterranea a ranar Alhamis da ta gabata.
Har ila yau dakarun tsaron gabar tekun na Libiya da na Italiya sun samu nasarar kubutar da bakin haure 1,500 daga halaka a tekun na Mediterranea a jiya Juma'a 19 ga wannan wata na Mayu.
A bisa kididdigar Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya: tun daga farkon wannan shekara ta 2017 zuwa yanzu, bakin haure kimanin 43,000 ne aka samu nasarar kubutar da su daga halaka a tekun Mediterranea a kokarin da suke yi na kutsawa cikin kasashen yammacin Turai ta hanyar teku.