Duban 'Yan Kasar Congo Sun Gudu Daga Jihar Kasai
(last modified Sun, 21 May 2017 07:34:10 GMT )
May 21, 2017 07:34 UTC
  • Duban 'Yan Kasar Congo Sun Gudu Daga Jihar Kasai

Wani jami'in Jumhriyar Demokaradiyar Congo ya sanar da gudun dubun dubatan mutanan Jihar Kasai dake fama da rikici.

A yayin ganawarsa da tawagar Dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD, Mista Marc Manyanga Ndambu gwamnan jihar Kasai ya shaida cewa sama da fararen hula dubu 20 ne suka gudu zuwa kasar Angola daga cikin jihar sakamakon fadan dake faruwa tsakanin jami'an tsaron kasar da 'yan tawaye masu goyon bayan Kamuina Nasapu.

Ndambu ya kara da cewa baya ga wadanda suka gudu zuwa kasar Angolar, akwai wasu sama da dubu 10 da suka nemi mafuka a sassa daban daban na cikin kasar, komawar mutanan ga mahalinsu su kuma ci gaba da rayuwar su ta yau da kulun ya danganta ne da yadda aka samu sulhu gami da tabbatar da tsaron a jihar.

Sama da shekaru 20 kenan da gabashin kasar Demokaradiyar Congon ke fama da matsalar tsaro, bayan da kungiyoyin daban daban na yan tawaye suka rike shi a matsayin wani sansanin su.