Gwamnatin Gambiya Ta Kwace Dukiyar Tsohon Shugaban Kasar Yahya Jammeh
(last modified Tue, 23 May 2017 05:52:35 GMT )
May 23, 2017 05:52 UTC
  • Gwamnatin Gambiya Ta Kwace Dukiyar Tsohon Shugaban Kasar Yahya Jammeh

Gwamnatin kasar Gambiya ta kwace wasu kadarori da aka ce na tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ne da suka hada da wasu asusun ajiya na banki guda 86 da kuma wasu kadarori kimanin 131 a ci gaba da binciken da ake yi dangane da dukiyar tsohon shugaban.

Ministan shari'ar kasar Gambiyan Aboubacar Tambedou ne ya sanar da hakan inda ya ce gwamnatin ta sami umurnin kotu na ta kwace dukkanin kadarorin da aka san na tsohon shugaba Jammeh din ne da kuma na kamfanonin da suke da alaka da shi har zuwa lokacin da za a gama bincike.

Gwamnatin ta ce tsakanin shekarun 2006 zuwa 2016 tsohon shugaba Jammeh ya wuwure Dala Miliyan 50 daga babban Bankin kasar don amfani na kashin kansa ciki kuwa har da sayen wani jirgin sama da wani gida a Amurka da kuma motoci masu tsadan gaske.

Daga cikin kayayyakin da aka kwace din har da kamfanoni 14 da suke da sunan Yahya Jammeh ko kuma kamfaninsa mai suna KGI, baya ga dabbobi da kuma motoci da sauran kayayyakin alatu masu tsada na tsohon shugaban.

Yahya Jammeh dai yana kasar Guinea inda yake gudun hijira tun bayan da ya bar kasar sakamakon tilasta masa barin mulki da aka yi bayan ya sha kaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar a bara.