Wasu Yan Bindiga Rufe Da Fuskokinsu Sun Kashe Kiristoci 28 A Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20740-wasu_yan_bindiga_rufe_da_fuskokinsu_sun_kashe_kiristoci_28_a_masar
Wasu yan bindiga rufe da fuskokinsu sun kashe kiristoci 28 sun kuma raunata wasu 25 a wani harin da suka kai masu a kudancin kasar Masar a safiyar yau jumma'a.
(last modified 2018-08-22T07:00:09+00:00 )
May 26, 2017 11:05 UTC
  • Wasu Yan Bindiga Rufe Da Fuskokinsu Sun Kashe Kiristoci 28 A Masar

Wasu yan bindiga rufe da fuskokinsu sun kashe kiristoci 28 sun kuma raunata wasu 25 a wani harin da suka kai masu a kudancin kasar Masar a safiyar yau jumma'a.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto wanda ya ganewa idanunsa yana cewa kiristocin wadanda suke wata tafiya ta ibada a cikin tawagar motocinsu a lokacinda yan bindigan suka tsare su suka kuma bude masu wuta suka kashe na kashewa suka tafi.

Shugaban kasar masar Abdul Fatah Sisi ya kira taron gaggawa na majalisar tsaron kasar don tattauna wannan batun. Wata tashar television na gwamnatin kasar ta nuna wata motar Bus wacce jini ya kwarara a cikinta da kuma alamun hoje hujen albarusai a inda abin ya fasru.

Shugaban Jami'an al-azhar Sheikh Ahmad Attayyeeb, wanda a halin yanzu yake ziyarar aiki a kasar Jamus ya yi All..wadai da harin ya kuma yi kira ga al-ummar kasar masar su hada kai don fada da ayyukan ta'addanci.