Wasu Yan Bindiga Rufe Da Fuskokinsu Sun Kashe Kiristoci 28 A Masar
Wasu yan bindiga rufe da fuskokinsu sun kashe kiristoci 28 sun kuma raunata wasu 25 a wani harin da suka kai masu a kudancin kasar Masar a safiyar yau jumma'a.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto wani da ya ganewa idanunsa yana cewa kiristocin suna cikin wata tafiya ta ibada ce a cikin tawagar motocinsu a lokacinda yan bindigan suka tsare su suka kuma bude masu wuta suka kashe da dama daga cikinsu
Shugaban kasar masar Abdul Fatah Sisi ya kira taron gaggawa na majalisar tsaron kasar don tattauna wannan batun. Wata tashar television ta gwamnatin kasar ta nuna wata motar Bus wacce jini ya kwarara a cikinta sannan akwai alamun hoje hujen albarusai a jikin motar ta kiristocin.
Shugaban Jami'an al-azhar Sheikh Ahmad Attayyeeb, wanda a halin yanzu yake ziyarar aiki a kasar Jamus ya yi All..wadai da harin ya kuma yi kira ga al-ummar kasar masar su hada kai don fada da ayyukan ta'addanci.