Gwamnatin Masar Ta Sanya Sunan Shugaban Kungiyar 'Ikhwan' Cikin Jerin 'Yan Ta'adda
Gwamnatin kasar Masar ta sanya sunan shugaban kungiyar 'Muslim Brotherhood' ta kasar Muhammad Badie tare da wasu jagororin kungiyar cikin jerin sunayen 'yan ta'adda na kasar.
A wani rahoto da ta watsa, tashar talabijin din Al-Mayadeen da ke watsa shirye-shiryenta daga kasar Labanon ta bayyana cewar a hukumance gwamnatin kasar Masar din ta sanya sunayen wasu mutane 118 'yan kungiyar 'Ikhwanul Muslimin' ciki kuwa har da shugaban kungiyar Muhammad Badie cikin jerin sunayen 'yan ta'adda a kasar.
Rahoton ya ci gaba da cewa wannan bayani dai yana cikin wata sanarwa ce da gwamnatin ta buga biyo bayan hukuncin da kotun manyan laifuffuka ta birnin Alkahira, babban birnin kasar Masar din ta fitar kan wannan batu a watan Oktoban shekarar bara ta 2016.
A shekara ta 2013 ne dai gwamnatin Masar din ta haramta kungiyar ta "Ikhwan" da kuma bayyana ta a matsayin wata kungiya ta ta'addanci biyo bayan kifar da gwamantin 'yan Ikhwan din karkashin jagorancin hambararren shugaban Masar din Muhammad Morsi da sojoji karkashin jagorancin shugaban Masar din na yanzu Abdulfattah Al-Sisi suka yi da kuma ci gaba da tsare tsohon shugaban da sauran mukarrabansa.