Kishirwa Ta Kashe Bakin Haure 44 A Hamadar Nijar
A Jamhuriya Nijar an gano gawarwakin bakin haure 44 da kishirwa ta kashe a hamadar sahara a kokarinsu na shiga Libiya, a lokacin da motarsu ta lalace.
Galibin wadanda suka rasun yan asalin kasashen Najeriya da Ghana ne da suka hada da jarirai uku, yara yan samari biyu da kuma mata 17.
Mutane shida daga cikin 50 da suka tsira daga lamarin ne suka kai labarin ga hukumomin garin Dirku dake iyaka da kasar Libiya.
Malam Lawal Taher wani dan kungiyar fara hula a garin na Dirku dake arewacin jamhuriya Nijar ya tabbatarwa da sashen hausa na muryar jamhuriya musulinci ta Iran da labarin inda ya ce mutanen na kokarin shiga Libiya ne don isa kasashen turai.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da irin hakan take faruwa ga bakin haure a hamadar sahara Nijar duk da matakan da hukumomin kasar ke cewa suna dauka don dakile wannan matsala ta safara bakin haure.