Mogherini: Tarayyar Turai Za Ta Ci Gaba Da Mutunta Yarjejeniyar Paris
(last modified Mon, 05 Jun 2017 06:38:15 GMT )
Jun 05, 2017 06:38 UTC
  • Mogherini: Tarayyar Turai Za Ta Ci Gaba Da Mutunta Yarjejeniyar Paris

Babbar jami'a mai kula da harkokin siyasar wajen tarayyar turai Federica Mogherini ta jaddada cewa, tarayyar turai za ta ci gaba da yin aiki da yajejeniyar Paris kan shawo kan matsalar dumamamar yanayi.

Mogherini ta bayyana hakan ne a jiya a lokacin da take halartar taron shugabannin kasashen kungiyar bunkasa harkokin tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma ECOWAS a birnin Monrovia na kasar Liberia.

Inda ta ce tarayyar turai tare da tarayyar Afirka, za su ci gaba da yin aiki kafada da kafada wajen aiwatar da wannan yarjejeniya, domin hakan amfanin dukkanin al'ummomin duniya ne.

Yarjejeniyar Paris da kasashen duniya suka rattaba hannu a kanta a karshen Disamban 2015, na da nufin tunkarar matsalar dumamar yanayi a duniya, yarjejeniyar da shugaban Amurka Donald Trump yasa kafa ya yi fatali da ita.