Burundi Ta Zargi (EU) Da Neman Tayar Mata Da Zaune Tsaye
(last modified Tue, 06 Jun 2017 05:47:48 GMT )
Jun 06, 2017 05:47 UTC
  •  Burundi Ta Zargi (EU) Da Neman Tayar Mata Da Zaune Tsaye

Mahukuntan kasar Burundi sun zargi kungiyar tarayyar Turai (EU) da neman tayar da zaune tsaye a cikin kasarta.

Wannan na zuwa ne, bayan da gwamnatin Burundin ta ce ta bankado wasu muhimman takardu dake nuna hannun kungiyar damu-damu a kokarin wargaza kasar.

Kakakin gwamnatin Burundi Philippe Nzobonariba ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, muhimman takardun, da wasu gamsassun bayanai marasa dadin ji sun nuna tsoma hannun tawagar kungiyar ta EU da suka ziyarci kasar a shekarar 2014, watanni da dama kafin tashin hankalin da ya barke a cikin kasar da kuma juyin mulkin kasar na shekarar 2015 da bai yi nasara ba.

Nzobonariba ya kara da cewa, muhimman bayanai sun kuma nuna cewa, kungiyar ta dauki nauyin wasu mutane da kungiyoyi domin su wargaza kasar, wadanda a halin yanzu ma'aikatar shari'ar kasar ta mika sammacin kasa da kasa domin a damke su.

A cewarsa, wadannan muhimman bayanai da sauran hujjoji, su ne suka tilasta wa mahukuntan kasar sanar da cewa, akwai hannun ketare a yunkurin yiwa zaben kasar na shekarar 2015 zagon kasa.