Amurka Ta Gargadi 'Yan Kasarta A Masar
Ofishin Jakadancin Kasar Amurka A Masar Ya Gargadi 'Yan Kasar sa Dangane Da Hare-Haren Ta'addanci
A cikin wata Sanarwa da ya fitar a wannan Talata, Ofishin Jakadancin kasar Amurka dake birnin Alkahira ya bukaci 'yan kasar dake son yin bulaguro zuwa kasar ta Masar da kuma wadanda suke zaune a kasar su dauki matakin taka tsatsan wajen guraren da suke shiga domin kaucewa hare-haren 'yan ta'adda.
Har ila yau Ofishin ya tabbatar da cewa duk wata ganawa da ma'aikatan Diplomasiyar kasar ke yi a wuraren addini a wajen birnin Alkahira, an dakatar da shi har zuwa wani lokaci.
A kwanakin baya dai an kai hare-haren ta'addanci a majami'ar mabiyar Addinin Kirista a kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama.