Gwamnatin Maroko Ta Bayyana Matsayinta Kan Boren Al'ummar Arewacin Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21092-gwamnatin_maroko_ta_bayyana_matsayinta_kan_boren_al'ummar_arewacin_kasar
Ministan harkokin cikin gidan kasar Maroko ya sanar da cewa: Gwamnatin kasar babu wani mataki da ta dauka na murkushe boren al'ummar arewacin kasar banda kokarin tabbatar da doka da oda.
(last modified 2018-08-22T07:00:13+00:00 )
Jun 07, 2017 02:06 UTC
  • Gwamnatin Maroko Ta Bayyana Matsayinta Kan Boren Al'ummar Arewacin Kasar

Ministan harkokin cikin gidan kasar Maroko ya sanar da cewa: Gwamnatin kasar babu wani mataki da ta dauka na murkushe boren al'ummar arewacin kasar banda kokarin tabbatar da doka da oda.

A jawabin da ya gabatar a gaban Majalisar Dokokin Kasar a jiya Talata: Ministan harkokin cikin gidan kasar Maroko Abdul-Wafi Laftit ya bayyana cewa: Tun bayan bullar boren al'ummar arewacin kasar, jami'an tsaron Maroko sun kame mutane kimanin 40 da nufin wanzar da doka da oda.

Abdul-Wafi ya kara da cewa: A halin yanzu haka gwamnatin Maroko ta dauki duk matakan da suka dace domin ganin ta kyautata rayuwar al'ummar yankin arewacin kasar musamman a fuskar tattalin arziki, zamantakewa da raya kasa.

Boren al'umma ya kunno kai ne a garin Al-Hoceima da ke shiyar arewacin kasar Maroko tun bayan da jami'an 'yan sandan kasar suka kashe wani mai sayar da kifi lamarin da ya rikide zuwa tarzomar neman hakki musamman kokawa kan matsalolin talauci, rashin aikin yi, barnata dukiyar kasa da sauransu.