Nijar Ta Kira Jakadanta A Qatar Don Tuntuba
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21184-nijar_ta_kira_jakadanta_a_qatar_don_tuntuba
Gwamnatin Nijar ta ce ta kira jakadanta a birnin Doha don tuntuba, biyo bayan rikicin diflomatsiya na tsakanin kasar Qatar da kasashe makoftanta larabawa na yankin tekun Pasha.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Jun 10, 2017 05:50 UTC
  • Nijar Ta Kira Jakadanta A Qatar Don Tuntuba

Gwamnatin Nijar ta ce ta kira jakadanta a birnin Doha don tuntuba, biyo bayan rikicin diflomatsiya na tsakanin kasar Qatar da kasashe makoftanta larabawa na yankin tekun Pasha.

Wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar, ta ce Nijar din ta yi hakan ne domin nuna goyan bayanta ga kasar Saudiya da kawayenta wadanda suka yanke duk wata irin hulda da Qatar bisa zargin taimakawa ayyukan ta'addanci.

Shafin yada labarai na Actuniger wanda ya rawaito labarin ya ce wannan matakin bai zo da mamaki ba kasancewar a jajibirin wannan rikicin, shugaba Isufu Mahamadu  ya yi wata ganawa da jakadan Saudiya a birnin Yamai na kasar ta Nijar.

Duk da cewa alakr dake tsakanin Saudiyya da Nijar tayi nisa data tsakaninta da Qatar, aman kasar ta Qatar na zamen babbar abokiyar hulda da Nijar din, inda ko a watan Fabrairu daya gabata, shugaba Isufu ya kai wata ziyara a birnin Doha inda kasar ta Qatar ta taimaka nijar da makuden kudade na aiwatar da wasu ayyukan ci gaba.

Kafin hakan kuma dama sarkin na Qatar Sheikh Hamad Khalifa Al-Thani ya ziyarci kasar ta Nijar, wanda hakan ya sa ake ganin matakin da Nijar din ta dauka baiyi tsauri ba kamar na sauren kasashen Afrika da tun tuni suka yanke alakarsu da kasar ta Qatar.