Gargadi Akan Fadawar Mutanen Habasha Cikin Matsala Saboda Fari.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun yi gargadin cewa; Kasar ta Habasha Za ta fuskanci matsanancin yanayi saboda farin da ta ke fama da shi.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun yi gargadin cewa; Kasar ta Habasha Za ta fuskanci matsanancin yanayi saboda farin da ta ke fama da shi.
Kamfanin Dillancin labarun Reuters ya ambato wasu kungiyoyin kare hakkin bil'adama da dama da ya kunshi cewa; Da akwai mutane miliyan 7 da dubu dari takwas a cikin kasar ta Habasha da su ke fama da karancin abinci.
Gargadin ya kuma kunshi yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su taimakawa kasar ta Habasha da gaggawa, idan kuma ba su yi ba, to nan ba da jimawa duniyar za ta fara ganin yadda mutanen Habashan za su rika mutuwa saboda yunwa.
A shekarun baya, kasar ta Habasha ta fuskanci fari wanda ya jaddasa mutuwar dabbobi masu yawa.