Sarkin Morocco Ya Bayar Da Umarnin Aikewa Da Abinci Zuwa Qatar
Jun 13, 2017 06:51 UTC
Sarkin Morocco ya bayar da umarnin aikewa da abinci zuwa kasar Qatar, wadda ke fuskantar takunkukumi daga kasashen larabawa da ke sayar mata da abinci.
Kamfanin dillancin labaran Jamus ya bayar da rahoton cewa, da jijjifin safiyar yau Talata, ma'aikatar harkokin wajen Morocco ta sanar da cewa, sarki Muhammad na shida ya bayar da umarnin aikewa da abinci zuwa Qatar, kamar yadda musulunci ya yi umarni kan musulmi su taimaka ma musulmi 'yan uwansu musammana cikin wanann wata mai alfarma.
A jiya gwamnatin Morocco ta sanar da cewa, a shirye take ta shiga tsakani domin sasanta rikicin da ya kunno kai a tsakanin Saudiyya da kawayenta da kuma Qatar a daya bangaren.
Tags