Ruwan Sama Ya Kashe Mutane 9 A Nijar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21356-ruwan_sama_ya_kashe_mutane_9_a_nijar
Hukumomi a Nijar sun ce mutane tara ne galibi yara suka rasa rayukansu sakamakon ruwa sama tamakar da bakin kwarya da aka samu a Yamai babban birnin kasar a cikin daren Talata zuwa Laraba data gabata.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Jun 16, 2017 05:49 UTC
  • Ruwan Sama Ya Kashe Mutane 9 A Nijar

Hukumomi a Nijar sun ce mutane tara ne galibi yara suka rasa rayukansu sakamakon ruwa sama tamakar da bakin kwarya da aka samu a Yamai babban birnin kasar a cikin daren Talata zuwa Laraba data gabata.

Bayanai daga kasar sun ce mai yiwa adadin mutanen ya zarta hakan, kasancewar rashin samun labarin wasu mutane, a yayin da kuma aka samu wasu gomman mutane da suka jikkata ciki har da masu munanen raunuka.

Galibin dai wadadan iftila'in ya rusa dasu bangwaye ne ko gidaje suka rufta akansu. 

Wasu rahotanni na daban sun kuma ce ambaliyar ruwa da aka samu ta haddasa hasara mai yawa wacce ta shafi gine-gine gwamnati, kasuwanni da kuma gidajen jama'a.

Tuni dai hukumomin kasar hadin gwiwa da abokan hulda da kungiyoyin agaji suka fara wani shiri na tantance yawan hasara da aka samu da kuma rajistar wadanda lamarin ya shafi domin taimaka masu a cikin gajerin lokaci.