Mali Ta Jaddada Aniyarta Ta Yaki Da Tsatsauran Ra'ayi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21374-mali_ta_jaddada_aniyarta_ta_yaki_da_tsatsauran_ra'ayi
Gwamnatin kasar Mali ta jaddada aniyarta ta shiga kafar wando daya da kungiyoyin masu tsatsauran ra'ayi a kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:15+00:00 )
Jun 17, 2017 02:37 UTC
  • Mali Ta Jaddada Aniyarta Ta Yaki Da Tsatsauran Ra'ayi

Gwamnatin kasar Mali ta jaddada aniyarta ta shiga kafar wando daya da kungiyoyin masu tsatsauran ra'ayi a kasar.

Kamfanin dillancin labaran France Press ya bayar da rahoton cewa, a yamamcin jiya ministan harkokin wajen kasar Mali Abdullahi Diop ya kirayi kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya domin amincewa da kudirin tarayyar Afirka na kafa rundunar yaki da ta'addanci a fadin nahiyar Afirka.

Ya ci gaba da cewa kasarsa tana daga cikin kasashen Afirka da suka fuskanci matsalolin tsaro daga kungiyoyin masu tsatsauran ra'ayin addini da ke aikata ta'addanci musamman a  arewacin kasar, amma duk da haka kasarsa ba ta taba yin kasa  a gwiwa ba wajen yaki da su.

Ya kara da cewa, kudirin tarayyar Afirka na kafa rundunar yaki da ta'addanci a nahiyar Afirka ya kara ma Mali azama wajen ci gaba da saka kafar wando daya da wadanann kungiyoyi.