Harin Bam Ya Hallaka Dan Sanda Guda A Birnin Alkahirar Masar
Bam ya tashi a kudancin birnin Alkahira na kasar Masar, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar jami'in dan sanda guda tare da jikkata wasu 4 na daban
Tashar Telbijin din Sky News ta nakalto Ma'aikatar tsaron Masar a wannan Lahadin na cewa Wani Bam da aka dasa a bakin hanya ya tarwatse, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wani babban jami'in 'yan sanda tare da jikkata wasu hudu na daban.
Ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, saidai akwai kungiyoyin 'yan ta'addar da suka yi mubaya'a da kungiyar Ta'addancin nan ta ISIS a kasar ta Masar daga cikin har da Velayatu-Sina sun jima suna kai irin wadannan hare-hare a kasar , kuma ya zuwa yanzu sun kadamar da dariruwar hare-haren ta'adanci a kan jami'an tsaro da suka hada da Sojoji gami da 'yan sanda a kasar ta Masar