'Yan Gudun Hijira Musulmi Na Kasar Afirka Ta Tsakiya Na Fuskantar Matsaloli
Maja'miar garin Bangaso ta sanar da cewa musulmi 1500 da su ke zaman gudun hijira a cikinta, suna fuskantar karancin abinci
Maja'miar garin Bangaso ta sanar da cewa musulmi 1500 da su ke zaman gudun hijira a cikinta, suna fuskantar karancin abinci.
Tashar telbijin din al-jazeera ta bada labarin cewa barkewar wani sabon rikicin a tsakanin kungiyoyin musulmi da kiristoci ya jawo kwararar dubban 'yan gudun hijira.
'Yan kungiyar "Anti Balaka' ta mabiya addinin kirista sun kai hari a masallacin garin " Bangaso" inda su ka kashe limami da masu salla.
'Yan gudun hijirar musulmi da su ke cikin cocin garin na Bangaso,suna fuskantar karancin abinci saboda yadda kungiyar ta "Anti Balaka" ta hana akai musu agaji.
Kakakin dakarun tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya velademir Mantiro, ya ce; Babu aminci akan hanyar cocin idan ace musulmin za su so fitowa.