Nijar : An Soma Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Zagaye Na Biyu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2152-nijar_an_soma_yakin_neman_zaben_shugaban_kasa_zagaye_na_biyu
A Jamhuriya Nijar yau Talata ne aka shiga yakin neman zaben shugabhan kasa a zagaye na biyu da za'ayi a ranar 20 ga watan nan tsakanin shugaba mai barin gado Mahamadu Issufu da abokin hammayyarsa Hama Amadu dake tsare a gidan kurkuku.
(last modified 2018-08-22T06:57:57+00:00 )
Mar 08, 2016 12:31 UTC
  • Hama Amadu da Mahamadu Issufu
    Hama Amadu da Mahamadu Issufu

A Jamhuriya Nijar yau Talata ne aka shiga yakin neman zaben shugabhan kasa a zagaye na biyu da za'ayi a ranar 20 ga watan nan tsakanin shugaba mai barin gado Mahamadu Issufu da abokin hammayyarsa Hama Amadu dake tsare a gidan kurkuku.

Wannan na zuwa ne bayan kotun tsarin mulki kasar ta amince da sakamakon zaben farko da aka gudanar a ranar 21 ga watan Fabrairun daya gabata.

babu dai wani sauyi na azo- a- gani da aka samu a tantancewar da kotun tayi game da sakamakon zaben da hukumar ta CENI ta bada tun da farko, illah wasu kura kurai na karin 'yan kuri'u ko ragewar su daga wannan jam'iyya zuwa wacen, koda yake kotun ta soke zabubukan wasu jihohi kasar Ghana.

Zaben ya shiga zagaye na biyu ne bayan Shugaba Mahamadou Issoufou na PNDS Tarayya mai shekaru 64 ya samu kashi 48.43% na kuri’u yayin da kuma Hama Amadou na Moden/Lumana mai shakaru 66 ya zo a matsayi na biyu da kashi 17.73.%

Za'a dai rufe yakin neman zaben ne a ranar 18 ga watan nan na Maris.