Tsohon Shugaban Kungiyar Ikhwanul Muslimin Mahdi Akif Ya Rasu A Cikin Kurkuku
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21850-tsohon_shugaban_kungiyar_ikhwanul_muslimin_mahdi_akif_ya_rasu_a_cikin_kurkuku
Tsohon shugaban kungiyar ikhwanul - muslimin ta kasar Masar ya rasu a cikin kurkuku
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Jul 02, 2017 06:06 UTC
  • Tsohon Shugaban Kungiyar Ikhwanul Muslimin Mahdi Akif Ya Rasu A Cikin Kurkuku

Tsohon shugaban kungiyar ikhwanul - muslimin ta kasar Masar ya rasu a cikin kurkuku

Tashar television ta Al-alam a nan Tehran ta nakalto wakilin kungiyar a birnin Alkahira Muntasar  Azziyaat  yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma kara ta cewa Mahdi Aakif ya rasu yana dan shekara 88 a duniya. 

Akif ya rike shugabancin kungiyar ne a shekara ta 2004 bayan rasuwar Mamin al-hudaibi, bayansa ne Mohammad Badee ya maye gurbinsa. 

Gwamnatin kasar masar ta yanzu dai ta yi amfani da karfin da wace misali kan y'ay'an kungiyar ta Ikhwanul muslimin sannan ta hana fursinoninsu samun magani ko ganin likitoci a lokacinda suke cikin gidan yari.

Aakif yana daga cikin fursononin da aka yenkewa hukuncin daurin rai da rai bayan juyin mulki, da kuma rikicin da suka biyo bayan rikicin shekara ta 2013.