Hannun Kasar Faransa A Kisan Kiyashin Da Aka Yi A Kasar Ruwanda
Bayan shudewar tsawon shekaru 23 da faruwar masifar kisan kiyashin da aka yi wa jinsin bil-Adama a kasar Ruwanda, a halin yanzu dalilai da hujjoji suna kara bayyana kan hannun kasar Faransa a faruwar wannan masifa.
A wani sabon rahoto da aka bankado dangane da masifar kisan kiyashin da aka yi a kasar Ruwanda, yana nuni da cewa: Kasar Faransa tana da hannu dumu-dumu a kisan kiyashin da aka yi wa 'yan kabilar Tutsi sakamakon umurnin da fadar Elysee ta Faransa ta bai wa sojojin kasarta da suke cikin kasar Ruwanda kan su mallakawa 'yan kabilar Hutu makamai alhalin Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba takunkumin mallakar makamai kan kasar ta Ruwanda lamarin da ya bai wa 'yan kabilar Hutu mafiya rinjaye damar aiwatar da kashe-kashen gilla kan 'yan kabilar Tutsi.
Kisan kiyashin da 'yan kabilar Hutu suka yi wa 'yan kabilar Tutsi a kasar Ruwanda shi ne kisan gilla mafi muni da aka yi wa jinsin bil-Adama a tsakanin wannan shekaru, don haka ake kiransa da kisan gilla mafi girma a wannan karnin sakamakon aiwatar da kisan kiyashi kan jinsin bil-Adama da yawansu ya kai 800,000 zuwa 1,000,000 a cikin kwanaki 100 kacal daga ranar 7 ga watan Aprilun shekara ta 1994 zuwa tsakiyan watan Yulin wannan shekara, kuma wannan kisan kiyashi ya kara zama mafi muni ne sakamakon aukuwarsa a kan idon dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu na Majalisar Dinkin Duniya musamman kasar Faransa da na Belgium.
Faruwar wannan kisan kiyashi a kasar Ruwanda a shekara ta 1994 ya samo asali ne sakamakon harbo jirgin saman shugaban kasar dan kabilar Hutu Juvénal Habyarimana da aka yi a kusa da birnin Kigali fadar mulkin kasar a ranar 6 ga watan Aprilun wannan shekara, lamarin da ya haifar da bullar yakin basasa a kasar, inda 'yan kabilar Hutu mafiya rinjaye suka farma 'yan kabilar Tutsi da kisa ba ji ba gani, lamarin da ya kai ga kashe dubban daruruwan mutane maza da mata gami da tsofaffi da kananan yara, tare da kame daruruwan mata 'yan kabilar Tutsi a matsayin bayi ana musu fyade, kuma duniya tana gani babu wani matakin gaggawa da ta dauka domin shawo kan masifar musamman dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da suke cikin kasar, bilhasali ma kasar Belgium da tafi yawan sojoji a dakarun Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Ruwanda, ta dauki matakin janye sojojinta daga kasar bayan da rikicin ya ritsa da wasu daga cikinsu. Ita kuwa kasar Faransa ta dauki matakin kebe wani yanki ne a kasar ta Ruwanda a matsayin yanki mafi tsaro domin kare sojojinta daga duk wata matsala tare da samun damar karfafa 'yan kabilar Hutu kan tafka laifukan yaki, sakamakon haka shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame ya sha maimaita cewa; Kasar Faransa tana da hannu dumu-dumu a kisan kiyashin da aka yi a kasarsa, zargin da mahukuntan Faransa suke musantawa.
Kasar Faransa da ake zargi da hannu a kisan kiyashin kasar Ruwanda, har yanzu tana ci gaba da aiwatar da bakar siyasarta ta mulkin mallaka kan kasashen da ta rene su a nahiyar Afrika, inda har yanzu take ci gaba da tatsarsu ta hanyar wawushe tarin arzikin da suka mallaka da rashin sakar musu mara domin juya akalar mulkin kasarsu ta hanyar ci gaba da jibge sojojinta a cikin kasashen da sunan tabbatar da tsaro. A fili yake cewa: Da kadan kadan tarihi zai ci gaba da bankado irin bakar siyasar mulkin mallaka da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen nahiyar Afrika da kasar Faransa ke yi.