Kafa Rundunar Hadaka A Arewa Maso Yammacin Afirka
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21910-kafa_rundunar_hadaka_a_arewa_maso_yammacin_afirka
Faransa tayi alkawarin taimakawa kasashen biyar na yankin Sahel domin kafa Rundunar hadin gwiwa ta yaki da 'yan ta'adda
(last modified 2018-08-22T07:00:20+00:00 )
Jul 04, 2017 14:20 UTC
  • Kafa Rundunar Hadaka A Arewa Maso Yammacin Afirka

Faransa tayi alkawarin taimakawa kasashen biyar na yankin Sahel domin kafa Rundunar hadin gwiwa ta yaki da 'yan ta'adda

A yayin ziyarar da kai kasar Mali, Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya dauki alkawarin taimakawa kasashen yankin sahel biyar a bangaren kafa Rundunar hadin gwiwa ta yaki da ta'addanci a yankin, inda ya ce Gwamnatin Faransa ta ware kayen aikin Soja da kimarsu ta kai Miliyan takwas na Euro da suka hada da motocin yaki guda 70 da za a raba su a tsakanin kasashen biyar na yankin Sahel.

A shekarar 2015 ne aka gabatar da shawarar kafa Rundunar hadin gwiwa ta yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda na yankin Sahel ganin yadda yankin ke fama da t'addanci na kungiyoyin 'yan ta'adda, saidai shawarar ta hadu da cikas saboda rashin kudi da Gwamnatocin yankin suka ce suna fama da ita,  kasashen biyar din na yankin Sahel da za su kafa wannan Runduna sun hada da Burkina Faso, Mali, Murtaniya, Niger da Tchadi.

Shugaban kasar Faransan dai ya ziyarci kasar ta Mali ne domin halartar taron da kasashe biyar din suka yi inda suka tattauna kan yadda za su kafa Rundunar hadin gwiwa ta yakin da kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin Sahel.