An Bukaci Daukan Mataki Na Kare Bakin Haure A Nijer
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21914-an_bukaci_daukan_mataki_na_kare_bakin_haure_a_nijer
Magabatan jihar Agadez dake arewacin jumhoriyar Nijer sun bukaci daukan kwararen matakai na kare bakin haure a yankin Sahara
(last modified 2018-08-22T11:30:20+00:00 )
Jul 04, 2017 18:51 UTC
  • An Bukaci Daukan Mataki Na Kare Bakin Haure A Nijer

Magabatan jihar Agadez dake arewacin jumhoriyar Nijer sun bukaci daukan kwararen matakai na kare bakin haure a yankin Sahara

Gidan Radion kasa da kasa na  Faransa ya habarta cewa cikin wata sanarwa da suka fitar mashawarta na babbar da'irar jihar Agadez 37 sun bukaci Gwamnati da ta dauki kwararen matakan tsaron domin kare 'yan gudun hijra na kasashen Afirka dake bi ta cikin kasar domin zuwa kasashen Turai.

Sanarwar ta ce a halin da ake ciki, hamadar Tenere na neman zama wata babbar makabarta na bakin haure, kuma wannan lamarin na zuwa ne tun bayan  da aka zartar da dokar nan ta hukunta masu safarar mutane da aka samar a shekarar 2015, kuma a halin da ake ciki, adadin bakin hauren dake rasa rayukansu a dajin hamada ya karu.

A cewar Muhamad Anakou, Shugaban Majalisar Mashawarta na jihar Agadez ,daga lokacin da aka fara zartar da wannan doka wacce ta bada damar yin hukunci mai tsanani ga wadanda aka kama da laifin safarar Mutane, masu wannan sana'a suka daina bin hanya domin kaucewa jami'an tsaro, lamarin da yake jefa su bin hanya mai hadari , wanda kuma daga karshe su da mutanan da suka dauka suke rasa rayukan su cikin Hamada.